Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

FRSC:za ta fara gwajin kwakwalwa ga masu tukin ganganci

Published

on

Hukumar kiyaye aukuwar hadura ta kasa FRSC ta ce da ga yazu duk wanda ta kama yana tukin da ya kauce tsari to la shakka sai an yi masa gwajin kwakwalwa.

 

Kwamandan rundunar reshen jihar Ogun Clement Olalede ne ya sanar da hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a yau Laraba a garin Ota.

 

A cewar sa dukkanin matukin da aka kama na kauce hanya ko kuma yana yin tuki ba yadda aka tsara ba musamman ma a yayin bukukuwan ista da ke karatowa, to za a tuhumeshi da laifin tukin ganganci.

 

Kwamandan ya ce irin wadan nan direbobo masu kunnen kashi, bayan wancan gwaje-gwajen na hauka za kuma su biya tarar naira dubu 50 ko kuma dauri a gidan yari.

 

Mr Oladele ya kara da cewa tuni hukumar ta fara shawagi a hanyoyin kasar nan, bisa karatowar biki Easter domin rage matsalolin da ake fuskanta a kan hanyoyin kasar nan.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!