Labarai
FRSC ta buƙaci direbobin da ke bin hanyar Abuja zuwa Kaduna su yi taka tsan-tsan

Hukumar kiyaye Afkuwar hadurra FRSC, ta bukaci direbobin da ke bin hanyar Abuja zuwa Kaduna da su yi hakuri tare da bin dokokin hanya sakamakon cunkoson ababen hawa da ake fuskanta yayin tafiye-tafiyen bukukuwan Babbar Sallah da kuma ayyukan gyaran hanya da ke gudana.
A cikin sanarwar da hukumar ta wallafa a shafinta na X a jiya Lahadi, ta bukaci matafiya da su kasance masu hakuri tare da kauce wa tukin ganganci domin rage hadurra da cunkoso a hanya. Ta kuma bayar da shawarar amfani da wata madadin hanya ga masu zirga-zirga tsakanin Kaduna da Abuja ta hanyar Kaduna–Kachia–Maraban Kubacha–Jere–Bwari–Dutse Abuja.
Haka kuma, hukumar ta sanar da fara aikin sintiri na musamman a fadin kasa domin bukukuwan Sallah na shekarar 2026, inda ta tura jami’ai sama da dubu 30 domin kula da hanyoyi daga ranar 25 zuwa 31 ga watan Mayu, da nufin rage hadurra da cunkoso tare da tabbatar da saukin zirga-zirga a kasar baki daya.
You must be logged in to post a comment Login