Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Gwamnatin Kano ta jadadda kudirin inganta kiwon lafiya

Published

on

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya jadadda kudirinsa na tabattar da an inganta harkokin lafiya a wani yunkurin inganta  harkokin kiwon  lafiya a matakan daban-daban na jihar Kano

 

Mataimakin Gwamna Alhaji Nasir Gawuna ne ya bayyana hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki a harkarkokin lafiya da aka gudanar na kwanaki uku da ya gudana a nan Kano.

 

Ya ce taron dai an gabatar da shi ne a lokacin da ya dace , duba da yadda yawan al’umma ke karuwa hakan ne ya zama wajibi a tabbatar da an inganta harkokin  lafiya yadda ya kamata.

 

Alhaji Yusuf Gawuna, ya kara da cewa tuni dai gwamnatin jihar Kano ta fara shirin tallafawa kiwon lafiya a matakin farko yayin da dubu dari uku da saba’in  mutane 370,000 suka ci gajiyar wannan shiri.

 

Yace Shirin tuni aka inganta shi tare da fara aiki a hukumomin kiwon lafiya  dari biyu da Arba’in da biyar  da  cibiyoyin lafiya  dari da Talatin da Hudu  sai manyan cibiyoyin lafiya  Talatin da bakwai  aka inganta su suka kuma  suke aiki  yadda kamata.

 

Mataimakin gwamnan Kano Alhaji Yusuf Gawuna ya  ce gwamnatin  dai har ila yau tuni ta fara aiwatar da shirin tara kudadden aiwatar da kiwon lafiya ga alummar jihar Kano, kamar yadda yake a kundin tsarin lafiya ta jihar Kano.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!