Connect with us

Labarai

Matatar Dangote ta sanar da rage farashin Fetur da Dizal

Published

on

Matatar Mai ta Dangote ya sanar da rage farashin fetur da Dizal da ga masu dillanci a kamfanin, a wani yunkuri na saukaka farashin man fetur da kuma tallafa wa harkokin tattalin arziki kasar nan.

Sabon farashin ya nuna cewa an rage farashin litar fetur daga naira 1,215 zuwa 1,165, wato an rage naira 50 kan kowace lita. Haka kuma, an rage farashin litar dizal daga naira 1,650 zuwa 1,570, wanda ke nuna ragin naira 80.

A cikin wata sanarwa da Kamfanin Dangote ya fitar a jiya Laraba, ya ce matakin na da nufin sauƙaƙa wa ‘yan Najeriya samun kayayyakin man fetur cikin sauƙi, tare da rage tsadar makamashi da kuma ƙarfafa ayyukan tattalin arziki.

Kamfanin ya ce rage farashin na nuna ƙudirin matatar wajen samar da ingantattun kayayyakin man fetur masu araha ga kasuwar Najeriya, tare da tabbatar da wadataccen mai a kowane lokaci.

Dangote ya kuma bayyana cewa zai ci gaba da rage farashi idan yanayin kasuwa ya ba da dama, yana mai cewa matatar na taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa tsaron makamashi a Najeriya da rage dogaro da shigo da man fetur daga ƙasashen waje.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!