Labaran Kano
Kungiyar kishin al’ummar Kano za ta gina cibiyar fasaha
Kungiyar Kishin al’ummar jihar Kano ,ta Kano Concerned Citizens Initiative ta KCCI, ta sanar da shirin ta na kafa wata babbar farfajiya ta fasaha da za’a rika kira ta da “Technology Village’’.
Matasa da suke da ilimin sarrafa kwamfuta da kwarewa a harkokin Internet za su baje fasahar su wanda zai bunkasa tattalin arzikin jihar nan.
Da yake jawabi a taron manema labarai a jiya Talata a cibiyar ‘yan Jaridu ta jiha shugaban kungiyar ta KCCI,Alhaji Bashir Usman Tofa ya bayyana wasu daga cikin matsalolin da tattalin arzikin kasar nan ke fuskanta, wanda shi tushen rashin aikin yi na matasa.
Alhaji Bashir Usman Tofa yace sun gana da matasa da suka kammala makaranta da sauran wadanda suka kware a bangaren ICT yayin da suka bayar da shawarar a kafa cibiyar sarrafa fasaha a nan Kano da wasu jihohin Arewacin kasar nan don samarwar matasa aikin yi.
Haka zalika Alhaji Bashir ya kara da cewar matasan maza da matan wanda suka kirkiri fasaha, amma abun takaici ne basu da jari.
Rahotanin sun bayyana cewar, a shekarar da ta gabata datijjan jahar ya gana da masu kirkira wanda suka yi bajakolin abubuwan da suka kirkira da suka hada jirgi mai saukar ungulu da mota da sababbin hanyoyin yin fanfonan burtsatse da kuma kayayyakin ayyukan gona da dai sauran su.