Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Mahaifiya ta hallaka jaririnta a Kano

Published

on

Jami’an sintiri na yankin Kawon Arewa dake nan Kano sun cafke wata mata mai suna Aisha Muhammad bisa zargin ta da kasha jaririn da ta Haifa.

Wata matashiya ce dai ta fara tona labarin bayan da ta shiga gidan inda ta iske gawar jaririn, daga nan ne jama’a suka taru, har ta kai ga jami’an sintirin yankin sun shigo ciki.

Sai dai a nata bangaren Aisha Muhammad ta bayyanawa wakilin mu Aminu Abdu Baka Noma cewa ta haifi wannan jariri sannan ba kashe shi tayi ba, Kazalika ba kuma kin sa take yi ba, illa ajali ne kawai yayi kira, sannan dan ta haife shi ne ba tare da aure ba.

Ita ma mahaifiyar Aisha ta tabbatarwa da Freedom Radio faruwar al’amarin inda ta ce makocin su ne yaci amanar su ya yiwa ‘yar ta ciki, amma tana rokon jami’an sintirin da su kashe maganar iya nan wurin.

Sakataren ‘yan sintiri na yankin Kawon Arewa Mallam Shehu Adamu ya bayyana cewa tun bayan da suka samu labarin ne suka je gidan sannan suka taho da yarinyar da mahaifiyarta da gawar jaririn kuma zasu mika su ga jami’an tsaro domin cigaba da bincike akai.

Rubutu masu alaka:

Mahaifiyar Siasia ta shaki iskar ‘yanci

Magidanci ya saduda ba yanda ya ga sunan Allah a jikin Doya

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!