Connect with us

Labarai

‘Yan yahoo sun damfari loba boy

Published

on

Wani matashi da ake kira da loba boy ya fada tarkon masu damfara a facebook, inda sukayi amfani da hotunan baturiya suka bude shafi da kuma sunan baturiyya watau Joy Dok.

Loba boy yace sun fara soyayya ne da ita zuwa wani dan lokaci inda daga bisani ta nemi da cewa zata turo masa kudi ta na’urar komfuta da kuma wayoyi domin su rika yin bidiyo suna ganin junan su.

Da yake maida maganar Loba boy ya ce  an  kira shi ne da safe  inda aka sanar da shi cewa kayan da wannan Baturiya ta aiko sun sauka a Jihar Lagos a filin jirgin sama na Murtala Muahammad.

An gurfanar da uba da ‘yarsa gaban kotu bisa zargin shirya auren bogi

‘Yan sanda sun kara ceto yara biyu da aka sace a Anambra

A cewar Loba Boy yace an bukace shi da ya karba ko ya tura kudin jirgi kimanin Naira 29,000 domin a turo masa da kayan  inda yake.

Bayan da aka kira shi Loba boy ya ce ya nemi rancen kudin kuma ya turawa wannan mutum da ya kira shi ta asusun shi.

Kazalika daga bisani  Loba boy ya gano cewa ba gaskiya a cikin al’amarin  inda yace bayan ya tura  kudin an kara neman sa daya tura wani kudin kimanin Naira 20,000  yayin da suka shaida  cewa jamian hukumar fasakwauri  sun kama wannan kayan nasa .

 

Labarai

Kai tsaye: Cigaba da bikin yaye daliban jami’ar tarayya ta Dutse

Published

on

Note: Ana cigaba da sabinta wannan shafi, ku cigaba da bibiya


Dalibai guda dari 786 ne jami’ar tarayya ta Dutsen jihar Jigawa, ke bikin yayewa a yau.

Rahotanin sun bayyana cewar, daga cikin dalibai dari bakwai da tamanin da shida (786) da ake bikin yayewa, hamsin da biyu (52) sun samu digiri mai matakin daraja ta farko wato First Class.

Kuma wannan shi ne karo na 5 da jami’ar ke bikin yaye dalibai.

Yanzu haka ana dab da kammala wannan biki da dake gudana a babban dakin taro na jami’ar.

A jawabin da ta gabatar, na yau Asabar shugabar jami’ar, Farfesa Fatima Batulu Muktar ta bayyana farin cikinta, tare da godiyar ta ga mahalarta taron inda ta bayyana irin nasarori da jami’ar ta samu musamman a bangaren ilimi da sauran bangarori na ci gaban jami’ar.

Farfesa Batulu Mukhtar ta kuma mika godiyar ta ga abokan hulda musamman gwamnatin jihar Jigawa da sauran dai-daikun al’umma da suka bada gudunmuwa wajen ci gaban jamiar.

Ku kalli hotuna daga wurin taron na yau:

Continue Reading

Labarai

Mata basu fiya karbar rashawa ba -Muhuyi Magaji Rimin Gado

Published

on

Gwamnatin jihar kano ta yi kira ga al’umma a ko wane mataki da su tashi tsaye domin yaki da cin hanci da rashawa ganin yadda matsalar ke kassara tattalin arzikin kasar nan.

Kwamishiyar mata ta jihar Kano Malama Zahra’u Umar ce ta yi wannan kiran ya yin wani taron bita da ma’aikatar kula da harkokin mata da hukumar karbar korafe korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar kano suka shirya don tattauna matsalolin dake addabar mata.

Malama Zahra’u ta kara da cewa mata suna da rawar da zasu taka wajen dakile ayyukan cin hanci da rashawa ta bangaren janyo hankalin mazajensu da su guji karbar na goro.

A nasa jawabin shugaban hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar kano Muhuyi Magaji Rimin Gado ya ce mata basu faya karbar cin hanci ba.

Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya ruwaito cewa mata da dama ne suka hallarci taron na wayar da kan mata akan cin hanci da rashawa.

 

Continue Reading

Labarai

Kamfanin NNPC ya tallafawa asibitin Aminu Kano

Published

on

Kamfanin mai na kasa NNPC ya baiwa Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano sabbin na’urorin dashen koda, zuciya, Hunhu da kuma hanji domin rage yawan ‘yan Nigeria dake zuwa kasashen ketare don yin dashen.

Karamin Ministan Mai nasa kasa Mele Kyari ne ya bayyana hakan a yau lokacin bikin kaddamar da sabbin kayayyakin dashen koda da zuciya da Kamfanin mai na kasa NNPC ya baiwa Asibitin koyarwa na Aminu Kano.

Mele Kyari wanda ya samu wakilcin Alhaji Abubakar Nuhu Muhammad ya ce sun dauki matakin ne domin takaita kwararar al’ummar Najeriya zuwa kasashen waje domin neman magani, inda ya ce hakan zai rage yawan kudin da ‘yan Najeriya ke kashewa a kasashen waje.

Abubakar Nuhu ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni da su rika tallafawa bangaren lafiya domin ceto rayukan masu karamin karfi.

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito cewa mutane da dama ne suka halarci taron kaddamar da sabbin kayayyakin da kamfanin NNPC ya baiwa Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano domin tallafawa al’umma baki daya.

Continue Reading

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!