Labarai
Tsuntsu ya kawo tsaiko kan tashin jirgin Habasha
Fasinjoji sun shiga halin-ni ‘ya-su bayan da wani tsuntsu ya kawo tsaiko wajen tashin su anan jihar Kano
Shigar wani tsuntsu cikin jirgin Saman Ethiopian airline ya tilastawa jirgin yin Zaman dabaro a filin jirgin Saman Malam Aminu Kano.
Rahotanni sun bayyana cewar jirgin yazo Kano ne domin diban ma tafiya zuwa birnin Adis Ababa, Amma sai aka ga wani tsuntsu ya kutsa ciki aka kuma nemi tsuntsun aka rasa.
Wannan ne yasa aka Dakatar da tashin jirgin domin Gano inda wannan tsuntsu ya shiga, daga bisani wata majiya ta shaida mana cewar an gano tsuntsun a cikin Injin jirgin lamarin da yasa ake jiran ma’aikata daga birnin Adis Ababa ko Abuja domin shawo Kan matsalar.
Najeriya ta rasa yan kasar ta guda biyu a hatsarin jirgin saman kasar Ethopia
Jigawa:mutane 19 ne suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin mota
Gwamnatin tarayya da wasu kasashen Afrika 22 sun dauke gabarar habbaka sufurin jiragen sama
Wakilin mu Nasiru Salisu Zango ya rawaito mana cewa tuni dai kamfanin jirgin ya samar da wurin kwana ga fasinjojin da jirgin ya taho dasu, wadanda za a diba a Kano kuma aka sallame su har zuwa lokacin da za a kammala gyaran jirgin.
Mun tuntubi kamfanin Ethiopian Airline dake Kano inda suka tabbatar da cewar hakika an Sami matsala a jirgin nasu, wanda ya tilasta hana shi tashi, sai dai basu yi cikakken bayani akan ainihin matsalar ba.