Labarai
DW na bada horo ga ‘yan jaridu a Abuja
An fara taron horaswa ga ‘yan jaridu akan makamar aiki a birnin tarayya Abuja, taron wanda Deutsche Welle ta shirya zai baiwa yan jaridun damar samun sabon salon hanyoyin kirkirar shiri a bangarorin dai-daitar jinsi, lafiya da sauransu.
Taron dai zai dauki tsawon kwanaki biyar ana gudanar da shi, zai kuma yi duba kan hanyoyin da yan jaridu zasu dauka wajen kayatar da shirye-shiryen su ba tare da masu sauraro sun fuskanci wani damuwa ba yayin saurara.
Haka kuma zai basu damar kara kaimi wajen gudanar da aiki.
Wakiliyar mu Samira Sa’ad Zakirai dake cikin mahalarta taron ta rawaito mana cewa masu horaswar daga makarantar horaswa na DW. Rudiger Maack da Mrs. Antje Bauer sun bayyana cewa, shirin zai baiwa yan jaridun damar bullo da sababbin hanyoyi mafi kayatar wa wajen gabatar da shiri.
Daga cikin kafafan yada labaran da ake horar da ma’aikatansu sun hadar da Freedom Radio Kano, Unity FM da Tincity FM daga jihar Plateau sai Rima FM da Caliphate FM daga Sokoto, Platinum FM daga jihar Nassarawa, Prestige FM daga jihar Niger, sai Progress FM daga jihar Gombe, Dandalkura Radio International daga jihar Borno, sai Bauchi Radio Cooperation daga jihar Bauchi, da kuma Liberty Radio daga birnin tarayya Abuja.
Rubutu masu alaka:
Fitacciyar ‘yar jarida Zainab Umar Ubale ta rasu
Gwamnatin Kano zata samar da Sabuwar shelkwatar hukumar Hisbah ta bayar da horo na musaman