Connect with us

Labarai

Ana zargin sarakunan mayun Kano na bogi ne

Published

on

Masu fashin baki  kan al’amuran yau da kullum sun bayyana cewar ofishin karbar korafe-kaorafe da yaki da cin hanci da karbar rashawa na jihar Kano karkashin shugabancin Barrister Muhyi magaji Riming ado,ta kawo karshen karyace-karyace da wasu ke yi da sunan Maita.

Masu bibiyar shafukan jaridu da na Internet idan suna biye damu a ‘yan kwanakin nan an t- kai-ruwa-rana dagane da yadda wasu masu yan dabaru ke amfani da  sunan maita ,har ma su dinga dora mutane a keken bera,karshe ma kaga an zo ana haddasa husuma a tsakanin mutane.

Rahotannin sun bayyana cewar, a kokarin dakile husumar ne ma yasa Anti corruption ta tashi haikan domin kawo karshen wnnan matsala, har ma aka kamo sarkin mayun Albasu da na Rege a karamar hukumar Wudil

Koda yake zuwan su hukumar sun ce ,kuskure aka samu domin dama can su ba mayu bane, kawai dai suna nutso da malafa ne domin samun abinci.

Wakilin mu Nasir Salisu Zango  a wancan lokaci ya zanta da fadar sarkin mayun Kano dake Gano,wanda a tattaunawar tasu yake cewar sudai wadannan sarakuna sune dai suke karya amma shi fadar su sun gaji maita kuma suna aikata ta.

 

Alhaji  Yahya Ali shine chiroman mayun Kano,na biyu mafi girman sarauta a fadar sarkin mayu dake garin Gano,ya hakikance akan cewar maitar tasu gaskiya ce.

Sarkin mayun boge ya karyata kansa

Mun kama Sarkin mayu na bogi-Muhiyi Magaji

Dole masu ruwa da tsaki su amince da hukuncin kotuna -Sarkin Kano

Sai dai a zantawar su dashi Nasiru Salisu Zango  y ace tun da dai ana magan ne akan tantance gaskiya ya roke shi da ya kama shi  alabasshi idan jiki sa  ya gaya masa sai a sake shi kaga Kenan sai ya idar kuma idan juna nan sa surutu gaba ya idar ya kuma cigaba da girmama wannan fada ta sarkin mayun Kano,a cewar Zango

Amma kuma  Zangon ya tabbatar da cewar Sarkin Mayun ya kasa kama shi kuma yaki aikata wani abu makamancin haka, wanda hakan ke nuni da cewar karya yake yi.

Har ila yau shima muyi magaji shugaban hukumar ta anti corruption ya bukaci chiroman na mayu wnada yake cewar yana kallon hanjin cikin mutane da ya gaya masa nau’in abin da yayi karin kumallo dashi ,nan ma dai aka yi tataburza.

Yanzu haka dai duka wadannan sarakunan mayu uku sun jadadda cewar dama can abin nasu ‘yan dabaru ne da nutso da malafa,sun kuma shaida cewar tun da sawun giwa ya taka na rakumi to sun zama sarakan tuwo da shayi maimakon sarakunan mayu.

Continue Reading

Labarai

Abinda ya sanya ‘yan adai-daita sahu janye shiga yajin aiki

Published

on

A yau jumu’a ne direbobin baburan adai-daita sahu na jihar Kano suka kudiri aniyar tafiya yajin aiki da kuma zanga-zanga, sakamakon harajin kudi har naira dubu ashirin da shida da hukumar KAROTA ta sanya musu.

Sai dai biyo bayan wani zaman sulhu da shugabannin kungiyoyin ‘yan adai-daitar sukayi da shugaban hukumar KAROTA an cimma matsaya, inda akayi yarjejeniyar cewa direbobin zasu biya naira dubu takwas-takwas kafin karshen watan disambar da muke ciki.

Tunda farko dai hukumar KAROTA ta kudiri aniyar rage yawan direbobin adai-daita sahun ne, ka sancewar sunyi yawa a gari fiye da kima, domin kuwa duk inda ka zaga, zaka hangi kalar ruwan dorawa irin ta baburan wadda kuma tayi kama da kayan sarki irin na jami’an Hukumar ta KAROTA.

Baya ga hakama dai hukumar KAROTA na zargin wasu daga direbobin na KAROTA na aikata wasu munanan laifuka.

Sai dai a karshe shuwagabannin ‘yan adai-daita sahun sun amince da janye yajin aikin da kuma zanga-zangar da suka shirya farawa a yau jumu’a, sai dai an jiyo wani tsagin kungiyoyin ‘yan adai-daita sahun na Kano na cewa suna nan akan bakansu, don haka basu gamsu da waccan maslaha ba kuma zasu tsunduma yajin aikin a yau.

Allah ya kyauta.

Labarai masu alaka:

Gwamanatin Kano za ta rage yawan baburan adaidaita sahu

Hukumar KAROTA ta nemi a kebe mata Naira biliyan guda

Continue Reading

Labarai

‘Yan sanda a Kano sun gargadi jama’a kan aikata laifi ranar bikin Maukibi

Published

on

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano gargadi al’umma, musamman bata gari da suke fakewa da lokacin taron jama’a domin aikata laifukan sara suka, da sauransu.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya rabawa manema labarai a daren yau, ya bayyana cewa rundunar ‘yan sanda ta shirya tsaf domin kula da shige da fice aranar Asabar mai zuwa da za’a gudanar da bikin maukibin waliyai da mabiya darikar Qadiriyya gabatarwa duk shekara a Kano.

DSP. Kiyawa ya bayyana cewa sunyi shiri na musamman domin zakulo wadanda suke fakewa da irin wadannan taruka su tayar da hankalin jama’a, a don haka suna gargadin al’umma dasu guji yin shigar banza, ko sanya kayan mata ko kuma yin wata shiga wadda ta saba da al’ada ko kuma addinin al’ummar jihar Kano.

Labarai masu alaka:

Rundunar ‘yan sandar jihar Kano ta sake ceto wani yaro a Anambra

Rundunar ‘yan sanda ta Kano ta yi holin masu yin garkuwa da mutane

Kazalika rundunar ‘yan sandan jihar Kano tayi shiri na musamman domin dakile masu ta’ammali da miyagun kwayoyi, da sara suka ko kwacen wayoyi da sauran laifuka a yayin gudanar da taron maukibi na bana.

Haka kuma rundunar ‘yan sandan jihar Kano na sanar da jama’a cewa har yanzu dokar nan tana nan ta haramta yin wani gangami ko zanga-zanga ko wani taron jama’a ba bisa ka’ida ba, kuma duk wanda ya karya wannan doka to babu shakka hukuma zatayi aiki akansa a cewar, kuma anyi hakan ne domin tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano a cewar DSP. Kiyawa.

A karshe rundunar ‘yan sandan ta taya al’ummar musulmi murnar zagayowar wannan wata da fatan za’a kammala bukukuwa lafiya.

Labarai masu alaka:

‘Yan film sun karrama kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano

Jihar Kano ta sami sabon kwamishinan ‘yan sanda

Continue Reading

Labarai

Ma’aikatan lantarki sun koma bakin aiki

Published

on

Kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa NUEE, ta janye yajin aikin sai baba ta gani da ta fara a jiya Laraba da nufin janyo hankalin gwamnatin tarayyar Najeriya kan hakkokin mambobinta.

Kungiyar dai ta sanar da janye yajin aikin ne da safiyar yau alhamis sakamakon wani zaman gaggawa da ta yi da jami’an gwamnatin tarayya.

Shugaban kungiyar ta NUEE na kasa kwamared Joe Ajaero ne ya tabbatar da janye yajin aikin ga manema labarai, yana mai cewa, sun tattauna matsalolin ma’aikatan sosai kuma gwamnatin tarayya ta yi alkawarin shawo kan matsalar.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, shiga yajin aikin kungiyar ya biyo bayan karewar wa’adin kwanaki 21 da ku kungiyar ta baiwa ministan lantarki Saleh Mamman, domin duba bukatun mambobinta, inda kuma rashin sauraron su da ya yi ne ya sanya su fara yajin aikin.

Continue Reading

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.