Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Kwankwaso mutum ne mai son kansa-Ganduje

Published

on

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje yace dabiar sa ta tabbatar da al’amuran rayuwa su kasance kamar yadda Allah yaso shi ne sanadin da yasa tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya samu cigaba a siyasa.

Gwamna Ganduje yace dabiarsa ta tabbatar da abubuwa sun tafi yadda ya kamata ya samo asali ne tun lokacin mulkin soja lokacin da aka zabi wadanda zasu wakilici Kano a majalisar tattauna tsarin mulkin Najeriya.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na yin wannan magana ce lokacin da yake karbar tsohon shugaban jamiyyar PDP Injiniya Rabiu Suleiman Bichi.

Bayanin na Gwamna Ganduje jaridar Solace base ce ta samo shi kamar yadda sakataren yada labarai na Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya fitar.

Gwamna Abdullahi Ganduje ya cigaba da cewa ko a zaben shekarar 1999 lokacin da sojoji zasu bayar da mulkii sun tsaya takarar fitar da gwani a jamiyyar PDP da tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso.

Gwamna Ganduje ya cigaba da cewa duk wadanda suka halacci zaben fitar da gwanin na gwamna a shekarar 1998 sun san cewa shi ya lashe zaben amma sai aka juyar da sakamakon domin Kwankwaso.

“Dalilin hakan ne yasa aka rarrashe ni in zama mataimakin tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso inda na hakura na karba da zuciya daya, daga baya sai Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya rika nuna min cewa kamar yayi min alfarma ne , na nuna masa cewa ba alafarma yake yi min ba illa naso a sake zaben fitar da gwanin ne”.

EFCC ta kwato kadarori 214 a hannun ‘yan siyasa da jami’an gwamnati

Hukumar INEC ta karyata zargin jam’iyyun siyasa na shrine daukar ma’aikatan N-Power

Gwamna Ganduje ya cigaba da cewa aje a tambayi Kwankwaso game da abunda ya faru tsakanin su, inda manyan yan siyasa irin su Alhaji Lili Gabari suka rarrashi shi Gwamna Ganduje.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yayi bayanai sosai irin matsalolin da ya fuskanta tsakanin sa da tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso inda yace shi da Injiniya Rabiu Suleiman Bichi sun san Kwankwaso sosai.

“Kai nine nake da kundun bayanai na waye Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ,kai nine Dikshinari na sanin waye Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ,kai banga mutum da yake da san kansa irin Inijiniya Rabiu Musa Kwankwaso ba, babu abunda ya sani sai kansa a duk abubuwan da yake yi.

Gwamna Ganduje yace yanzu babbar matsalar Kwankwaso a rayuwa shine mafarkin ya zama shugaban kasa ,shi yasa yake ta canja jam’iyyu daban daban kuma muna da labarin yana shirin dawo wa babbar jamiyyar mu ta APC  saboda yana ganin idan shugaba Buhari ya kammala wa’adin sa a shekarar 2023 zai iya zama shugaban kasa.

sama da jam’iyyun siyasa 100 ne za su shiga takara a zaben shekarar 2019-inec

Buhari, Zulum, Kwankwaso, El-Rufai- Wa Nigeria ta fi bukata a cikinsu?

Kai Kwankwaso bai yi farin ciki ba sanda Dr Abdullahi Umar Ganduje ya zama Gwamna a shekarar 2015 domin ko sau daya bai taba bina yakin neman zabe ba.

Kai ko kwabo bai bani ba a matsayin gudunmawar sa ta yakin neman zabe kai da na samu nasara a matsayin gwamnan jihar kano sai Injinya Rabiu Musa Kwankwaso ya fara nuna wasu halaye da basu kamata ba inji Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!