Connect with us

Manyan Labarai

Mun samu rahoton aikata ba daidai ba a wasu mazabu-Abdulmumini Jibrin.

Published

on

Daga Abdullahi Isa

Dan takarar jam’iyyar APC a zaben dan majalisar wakilai da ke gudana a yau a yankin kananan hukumomin Kiru da Bebeji, Abdulmumini Jibrin, Kofa, ya ce sun samu labarin aikata laifuffukan zabe a wasu daga cikin mazabun kananan hukumomin guda biyu.

Abdulmumini Jibrin wanda ke zantawa da manema labarai bayan ya kada kuri’arsa a cibiyar zabe ta Kai’lu da ke Kofa a yankin karamar hukumar Bebeji.

Idan ba’a farga ba  Yan siyasa zasu yi amfani da Almajirai a matsayin ‘’Yandaba- Sarki Sunusi II

Shugaba Buhari ya ja kunnen yan siyasa kan yakin neman zabe

”Magana ta gaskiya a wasu mazabun wakilanmu sun tabbatar mana cewa ana aikata abubuwa marasa dadi amma ba zamu ce komai ba kan wannan batu a yanzu sai nan gaba.” inji Abdulmumini Jibrin Kofa.

Sai dai ya ce ya gamsu da yadda zaben ke gudana a mazabar sa saboda komai ya wakana lami lafiya.

Freedom Rediyo ta gano cewa an samu karancin fitowar jama’a a da dama daga cikin mazabun da ke yankunan kananan hukumomin biyu.

Labarai

Amaechi ya karya ta labarin ya tsallake rijiyar da baya

Published

on

Ministan sufurin Rotimi Amechi ya karyata labarin da ake yadawa cewa ya tsallake rijiya da baya, bayan da masu satar mutane suka kaiwa jirgin kasa hari a Mando dake jihar Kaduna, da yammacin jiya Lahadi.

Rotimi Amechi ya wallafa hakan a shafin sa na Twitter cewa labarin karya ce tsagwaran ta, a don haka al’umma su yi watsi shi.

Rahotanni sun bayyana cewar, a jiya Lahadi ne masu satar mutane suka yi artabu da jami’an tsaro dai-dai lokacin da fasinjoji za su sauka a tashar jirgin kasa dake Rigasa.

Sai dai da safiyar yau ministan ya karya ta cewa yana cikin jirgin dai-dai lokacin da aka kai harin.

Wata majiya mai karfi daga tashar jirgin kasan ta Kaduna ta tabbatarwa da Freedom Radio afkuwar harin, amma bayan da ministan sufurin ya sauka daga jirgin kasar ne.

Labarai masu alaka:

Kotu tayi watsi da bukatar soke sabbin masarautu

Muhimman abubuwan dake faruwa yanzu haka a Kannywood

Continue Reading

Labarai

Kotu tayi watsi da bukatar soke sabbin masarautu

Published

on

Babbar kotun jihar Kano ta kori karar da masu zabar sarki na masarautar Kano suka shigar suna kalubalantar kirkirar sabbin  masarautu guda hudu da gwamnatin jihar Kano ta yi.

Da yake yanke hukunci a safiyar yau litinin, mai shari’a Ahmed Tijjani Badamasi ya kara tabbatar da hukuncin da mai shari’a Usman Na’aba ya yi a ranar 21 ga  watan Nuwamban shekarar da ta gabata na tabbatar da masarautun.

Majalisar dokoki ta Kano ta amince da dokar kafa masarautu 4

Ganduje ya sakawa dokar kikiro masarautu hannu

Kotu ta dage sauraran karar dattawan Kano kan sabbin masarautu

 

Idan za’a iya tunawa masu nada sarki a masarautar Kano wanda suka hada da Madakin Kano Hakimin Dawakin Tofa Yusuf Nabahani , da Makaman Kano kuma hakimin Wudil Abdullahi Sarki-Ibrahim da sarkin Dawaki Mai Tuta kuma hakimin Gabasawa Bello Abubakar da sarkin ban Kano hakimin Dambatta Muktar Adnan sune suka shigar da karar suna kalubalantar kirkirar sabbin masarautun.

 

 

 

Continue Reading

Manyan Labarai

Bana neman matar Aure-BABANGIDA

Published

on

Tsohon shugaban mulkin sojin kasar nan janar Ibrahim Badamasi Banagida mai ritaya, ya ce, shi kam baya neman wata matar aure.

A wata zantawa da yayi da jaridar Daily Trust, janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya, ya ce, shi ba ya bukatar yin aure a yanzu, saboda duk wata kulawa da ya kamata ‘ya’ya su yiwa mahaifinsu ‘ya’yan sa, na yi masa.

Ya ce, a yanzu  a matsayin sa na dattijo dan sama da shekaru saba’in, yana ga ba ya bukatar sai ya yi aure.

A baya-bayan nan ne dai, rahotanni su  ka yi ta yawo a kafafen yada labarai da ke cewa, tsohon shugaban mulkin sojin na neman matar aure.

A ranar 7 ga watan Disamban shekarar 2009 ne, mai dakin tsohon shugaban kasar, Hajiya Maryam Ibrahim Badamasi Babangida, ta rasu a wani asbiti da ke birnin Los Angles a jihar California da ke kasar Amurka bayan ta yi fama da cutar daji. Tun daga nan dai har ya zuwa yanzu, tsohon shugaban kasar, bai kara yin aure ba.

Continue Reading

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!