Labarai
Jami’an tsaro ku kama duk mai tunzura jama’a-Sarkin musulmi
Shugaban majalisar koli ta addinin musulunci kuma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bukaci jami’an tsaron kasar nan da su dauki matakin kama duk wami malamin addini da ke yada kalaman tunzura jama’a.
Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana hakan ne yayin wani taron zaman lafiya da kuma gina kasa, da majalisar Da’awah ta kasa ta shirya a garin Jos babban birnin jihar Plateau.
Ya ce, akwai bukatar a rika gudanar da harkokin addinai ta yadda za a kaucewa tada rikice-rikice.
Matsalolin aure: Sarkin Kano ya bukaci a koma makaranta
Abinda ya sa ban ce komai ba kan batun sanya Hijab a Jamia: Sarkin Musulmi
Sarkin musulmi ya bukaci gwamnatin tarayya ta zage dantse don magance matsalolin tsaro
Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya kuma yi kira ga kungiyar Jama’atu Nasril Islam da kungiyar Kiristoci ta kasa CAN da su yi dukkan mai yiwuwa wajen kawo karshen cece-kucen dake faruwa tsakanin mabiya addinan biyu a kafafen yada labarai.