Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

‘Yan wasa sun nemi hukuma ta biya su alawus

Published

on

Yan wasan tsalle -tsalle da guje -guje na kasar nan ,sun bukaci da hukumar wasannin ta kasa Athletic federation of Nigeria wato AFN, da ta biyasu kudaden Alawus ,Alawus da suke bi tun a lokutan baya ,karkashin jagorancin tsohon shugaban hukumar Alhaji Ibrahim Shehu Gusau.

Yan wasan dai sun nemi hakan ne a gasar gwaji na wasannin jami’ar Kere -kera ta tarayya dake Akure. Daga cikin kudaden da suka nema  a biya su ,sun hada da gasar wasannin nahiyar Afirka da aka gudanar a birnin Asaba na jihar Delta a shekarar 2018, da kuma gasar kasashen duniya ta hukumar wasannin tsalle tsalle da guje -guje na duniya IAAF, a birnin Yokohama na kasar Japan, dana birnin Doha na kasar Qatar a shaekarar data gabata wato 2019.

A baya dai ana rade radin cewar hukumar ta samu kudi kimanin dala dubu 92, da ga ma’aikatar wasanni ta kasa , wanda aka sa ran cewar kowanne dan wasa zai karbi dala 1,300.Sabon shugaban hukumar Mista George , ya baiwa yan wasan hakuri ,tare da alkawarta musu biyan su nan kusa ,kasancewar an saka kudaden nasu a cikin kasafin kudin bana.

A wasan Taekwando, Najeriya na fuskantar barazanar rashin zuwa wasannin share fagen shiga gasar wasannin motsa jiki na Bazara, a birnin Tokyo na kasar Japan a cikin shekarar nan , sakamakon rashin kudaden aiwatar da harkokin ‘yan wasan na Taekwando.

Wasannin wanda zasu gudana, a birnin Rabat na kasar Morocco, ya na da ‘yan wasa daga kasar nan Elizabeth Anyacho, mai wasan kilo 67, sai Chinazum Nwosu, mai wasan kilo 53, da Ife Ajayi mai wasan kilo 68, sai Benjamin Okoumose mai kilo 80, da mukarraban hukumar su Tara, da suka hada da mai horar wa John Victor , shugaban hukumar ta Taekwando Margret Binga, da sakataren hukumar Kabir Yusuf, na cikin tawagar da ake sa ran zuwan su Rabat, sai dai har zuwa lokacin rahoton suna nan a birnin tarayya Abuja.

Hakan tasa, in suka haura zuwa yau kasar nan ba fuskantar ficewa daga gasar ,sakamakon cewa za’a fara wasannin ranar Jumma’a 21, ga watan nan.

A yanzu dai Najeriya na bukatar dalar Amurka dubu 21, kimanin naira miliyan 8, don gudanar da shirye -shiryen da suka shafi gasar.

Daga gasar cin kofin zakarun nahiyar turai , dan wasan gaban kungiyar Atletico Madrid , Diego Costa zai samu damar buga wasan da kungiyar sa zata fafata da jagora teburin gasar firimiyar kasar Ingila kuma mai rike da kofin zakarun nahiyar Turai Liverpool, a wasan zagaye na biyu wato second round na gasar a yau.

Hakan dai ya biyo bayan doguwar jinyar da dan wasan ya yi daga rauni daya samu tun watan Nuwambar bara.

A bangare daya kuma dan wasan bayan kungiyar dan kasar Uruguay , Jose Giminez , shima ya dawo daga raunin da yayi jiyya ,in da zai shiga cikin tawagar da zata fafata a yau da Liverpool. Sai dai a wani koma baya ga kungiyar ta Atletico yan wasa Joao Felix, da Kieran Trippier ba zasu buga wasan ba sakamakon jinya ta raunin da suka samu.

Rahoto: Aminu Halilu Tudun wada

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!