Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kungiyar Kwallon kafa ta Jigawa Golden stars ta lalasa Wikki Tourist

Published

on

Kungiyar Kwallon kafa ta Jigawa Golden stars , ta samu galaba akan takwarar ta Wikki Tourist dake jihar Bauchi a wasan firimiya na kasa mako na 21,daya aka fafata a filin wasa na Sani Abacha dake unguwar Kofar Mata a yammacin yau.

Dan wasan kungiyar Wikki Promise Damala , ne ya fara saka Kwallo a ragar kungiyar ta Jigawa a minti na biyu na farko Rabin lokaci kafin kungiyar ta Jigawa , ta warware tare da kara Kwallo ta biyu data bata galaba akan kungiyar ta Wikki da ci 2 da 1.

Dan wasa Saleh Ibrahim mai lakabin Nasara, shi ne ya ramawa kungiyar ta Jigawa Kwallo a minti na 54, Jim kadan bayan dawowa daga hutun Rabin lokaci, ya yin da Abdullahi Lala, ya zura Kwallo ta biyu data baiwa kungiyar ta sa ta Jigawa nasara a wasan a minti na 67.

Da yake jawabi Jim kadan bayan tashi daga wasan, mai horar da kungiyar ta Jigawa Gilbert Opana, ya yabawa ‘yan wasan sa da kokarin da suka nuna, sai dai ya caccaki Alkalin wasan da ya busa wasan da cewar busar sa cike take da kura kurai.

‘Yan wasa sun nemi hukuma ta biya su alawus

Kano Pillars ta samu nasara karon farko a kakar wasanni ta bana

Kano Pillars ta lallasa Delta Force da ci 6-1

A nasa bangaren mai horar da kungiyar Wikki Tourist , Usman Abdallah, ya ce zasu duba matsalolin da suka fuskanta, tare da yawan rage kuskuren yan wasan sa don ganin sun samu gogewa a fannoni daban daban a cikin fili.

Ya yin da a can jihar Rivers , Kano Pillars tayi rashin Nasara da ci 2-1, a wasan data fafata da mai masaukin baki Rivers United , inda yan wasan Rivers Konan Ruffin Ngoun da Cletus Omatan, suka zura kwallaye a minti na 22 da 88, ana dab da za’a tashi a minti na 90, kyaftin din kungiyar Kwallon kafa ta Kano Pillars Rabiu Ali Pele, ya ramawa kungiyar da bugun tazara, wato freekick.

Sauran wasannin da suka gudana sun hada da.

MD 21,#NPFL20

Dakkada 0-0 Kwara Utd

MFM 0-0 Heartland

Nasarawa Utd 2-0 Enyimba
Chinedu Ohanachom 33’, Dauda Maigishiri 87’

Lobi Stars 0-0 Plateau Utd

Akwa Utd 1-1 Wolves
Ndifreke Effiong 90’ – Wisdom Jumbo 76’ (PEN)

Sunshine Stars 0-0 Rangers

Katsina Utd 1-0 Abia Warriors
Joseph Atule 6’

Adamawa Utd 2-1 FCIU
Jibrin Abubakar 22’, Idris Abubakar 69’ – Ikenna Cooper 67’.

Zuwa yanzu haka kungiyar Plateau United ke saman Teburin Jadawalin gasar da maki 37 bayan wasanni 21.

Rahoto daga,

Aminu Halilu Tudunwada.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!