Manyan Labarai
Kasar Saudiya ta dakatar da zuwa Umara
Kasar Saudi Arebiya ta dakatar da bayar da izinin shiga kasar wato Visa, ga masu niyyar zuwa kasar don yin Ibadar Umrah.
A cewar gwamnatin kasar wannan wani mataki ne na kokarin dakile yaduwar cutar Corona wadda aka canjawa suna Covid19.
Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da dubban musulumin duniya ke shirin zuwa gasar domin gudanar da ibadar Umara a watan azumin Ramadan.
Rahotanni sun ce, ya zuwa yanzu, ba a samu labarin bullar cutar a kasar ta Saudi Arebiya ba, sai dai an samu a makociyarta wato kasar Iran.
Masu lura da lamuran yau da kullum dai na ganin cewa, kasar ta Saudi Arebiya tana halin tsaka mai wuya, sakamakon cewa a watan Yuli za a fara shiga kasar domin gudanar da aikin Hajji.
You must be logged in to post a comment Login