Labarai
A bamu aiki ko mu koma bara-Makafin Kano
Kungiyar makafi ta jihar Kano sun gudanar da zanga-zanga lumana a nan Kano.
Zanga-zanagar ta fara ne daga ofishin ma’aikata zuwa majalisar dokoki na nan Kano ya dagana zuwa hukumar ilimin bai daya USBEB.
Makasudun wannan zanaga-zangar shi ne yadda shugaban hukumar ilimin bai daya Dan Lami Hayyu yaki sanya sunayen makafi cikin malaman da za’a dauka.
Su dai makafin na ikirarin cewar Dan lami Hayyu ba zasu iya koyar ba, kasancewar ana bukatar kwararru ne.
Sama da mutum 2,000 ne suka amfana da kayan masarufi na azumi da Hajiya Halima Shekarau ta raba
Matasa sun yi zanga-zanga kan aikin Titin Five Kilometer
Niger- Matasa sun yi zanga-zanga dangane da lalatattun tituna a Minna
Sai dai wakilin mu Yusuf Ali Abdullah ya tuntubi shugaban hukumar ilimin bai daya yana mai cewa baya gari yana jihar Katsina don gudunar da aiki, amma ya ce da zarar ya sami sarari zai neme mu, amma kawo lokacin da muke hada muku wannan rahoton bai ce komai ba.
Akan haka ne wakilin mu ya tuntubi ofishin shugaban ma’aikata na jihar Kano Dr, Kabiru Shehu, shi ma aka ce yana ganawa da sababin kwamishinoni, ba zai samu sukunin tattaunawa da mu.