Labarai
Yaran Kano: Majalisar dokokin Kano zata dauki mataki
Majalisar dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jiha da ta gaggauta daukan mataki tare da bibiyar sauran yara ‘yan asalin jihar Kano da har yanzu suke hannun wadanda suka sacesu a ka boyesu a jihar Anambra.
Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa da shugaban masu rinjaye na majalisar Abdul Labaran Madari ya gabatar yayin zaman majalisar na yau.
Majalisar ta kuma bukaci kungiyar jamaatu Nasril Islam da ta fito fili tayi Allawadai da sace yara a kano ana sauya musu addini.
Majalisar wakilai za ta kaddamar da shugabannin kwamitoci
Ko kun san me ya hana Ganduje nada Kwamishinoni?
Satar yaran Kano da munafurcin kafafan yada labarai
Haka zalika majalisar ta yabawa rundunar ‘yansandan jihar kano sakamakon kokarin da ta ce tayi wajen nasaran ceto yaran.
Bayan da gabatar da kudirin Abdul Labaran Madari ya kuma ce kamata yayi gwamnati Kano da ta gaggauta kafa kwamtin da zai bibiyi yadda za’a dawo da yaran a kuma sada su da iyalan su.
Daga bisani majalisar dokokin ta Kano ta amince da kudirin.