Manyan Labarai
A Kano ana magance cutar da kasar India ta kasa
Asibitin Muhammadu Buhari dake unguwar Giginyu na maganin cututtukan da aka kasa yi a kasar Indiya.
Shugaban asibitin Muhammadu Buhari dake unguwar Giginyu anan Kano Dr Garba Waziri Dahiru ne ya bayyana haka lokacin da yake tattaunawa da filin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio.
Dr Waziri Garba Dahiru yace tun fara aikin asibitin a watan Mayu na shekarar 2018 asibitin yayi wa wani dan jihar Kwara da ya fito daga garin Ilori aiki da ya gagari yi a kasar India.
Shugaban asibitin ya kara da cewa ana yin tiyatar kwakwalwa a asibitin na Muhammadu Buhari wanda wani likita dan asalin jihar Kano Dr Shuaibu Sule Dambatta yake jagoranta.
Shi dai Dr Shuiabu Sule Dambatta ya fito ne daga wani asibiti a kasar Ingila.
Dr Waziri Garba yace tun kafuwar asibitin na Muhammadu Buhari suna yin aikin tiyatar kwakwalwa a duk sati sau biyu.
Daga nan yace asibitin yana da gurin gaggawa mafi kyau na kula da marasa lafiya da cutar su tayi tsanani wato Intensive care unit.
Yayi kira ga al’umma da su cigaba da zuwa asibitin domin duba su inda yace al’umma da dama basu fahimci cewa za’a iya duba su a asibitin ba.