Connect with us

Labaran Wasanni

A karshen watan Satumba za’a gudanar da zabe a hukumomin wasanni na Najeriya-Sunday Dare

Published

on

Ministan matasa da wasanni na kasa Sunday Dare, ya ce a ranar 30 ga watan Satumbar shekarar da muke ciki ta 2021 ne za’a gudanar da zabe a hukumomin wasanni na kasar nan.

Hakan na cikin wata Sanarwa da hukumar ta fitar a ranar 8 ga watan satumbar da muke ciki.

Sanarwar ta ce hukumomin wasanni 6 ne ake saran za’a gudanar da zaben fitar da gwani na wadan da za su jagoranci hukumomin.

Zaben dai zai kasance ne a karkashin kulawar hukumar wasanni ta kasa.

Daga cikin hukumomin wasannin da za su fafata akwai hukumar kwallon kwando data hukumar kwallon zari ruga ta Rugby da ta Tennis da ta kwallon kafa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!