Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Kano pillars za ta yi wasan sada zuminci da Dabo Babes

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars mai taken Sai Masu Gida, za ta buga wasan sada zumuni da kungiyar kwallon kafa ta Dabo Babes da ke nan jihar Kano.

Dabo Babes dai na guda daga cikin kungiyoyin da suke taka rawar gani a wasannin da suke fafatawa a jihar.

Kano Pillars ta dakatar da daukar sabon mai horar wa

Wasan dai tsakanin Kano Pillars da Dabo Babes zai gudana  a ranar Asabar 11 ga Satumbar da muke ciki a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar Mata inda za’a buga wasan da misalin karfe 4:00 na yamma.

Kano Pillars a kakar wasannin data gabata ta kasance a mataki na biyar da maki 64 a gasar NFPL da kungiyar kwalllon kafa ta Akwa United ta lashe karon farko a tarihin ta.

Wanda kuma tuni kungiyar ta Sai Masu Gida ke shirin daukar sabon mai horarwa da zai jagorance ta a sabuwar kakar wasannin 2021/2022 da za’a fara nan gaba kadan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!