Labarai
A makon gobe za a fara binciken Hadiza Bala Usman kan zargin badakalar biliyan 165
A makon gobe ne ake sa ran kwamiti na musamman da gwamnatin tarayya ta kaa zai fara binciken dakatacciyar shugabar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta kasa Hadiza Bala Usman.
Rahotanni sun ce kwamitin zai gudanar da bincikensa ne kan zargin rashin sanya wasu kudade da hukumar ta tattara a asusun tarayya, wanda ya kai jimilar naira biliyan dari da sittin da biyar da miliyan talatin da biyu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ana sa ran kwamitin da ke karkashin jagorancin daraktan kula da harkokin teku na ma’aikatar sifiri zai kuma fadada binciken nasa kan kafatanin kudaden da hukumar ta samu tun lokacin da Hadiza Bala Usman ta fara jagorancin hukumar.
A baya-bayan nan ne dai shugaban kasa Muhamadu Buhari ya ba da umarnin dakatar da ita tare da kafa wani kwamiti na musamman don binciken ayyukanta.
You must be logged in to post a comment Login