Labarai
A watan Janairun 2022 za’a fara amfani da 5G Network a Najeriya-Pantami

Gwamnatin tarayya ta ce za’a fara amfani da tsarin 5G Network a kasar nan daga watan Janairun shekara mai kamawa ta 2022.
Ministan sadarwa da tattalin arziki Isa Ali Ibrahim Pantami, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis 23 ga watan Satumbar shekarar 2021, yayin da yake ganawa da manema labarai a garin Maidugurin jihar Barno.
Pantami ya ce tsarin zai taimaka, wajen rage barnatar da dukiyar da al’ummar kasar nan keyi a bangaren na sadarwa.
Pantami, ya ce a kwanan nan majalisar wakilan kasar nan ta amince da tsarin na 5G Network.
You must be logged in to post a comment Login