Labarai
Abdullahi Abbas bai cancanci shugabancin jam’iyya ba – Ɗan Sarauniya
Tsohon kwamishinan ayyuka na gwamnatin Kano Injiniya Mu’azu Magaji Ɗan Sarauniya ya soki shugaba jam’iyyar APC na Kano.
A wata hira da Freedom Radio Ɗan Sarauniya ya ce, Abdullahi Abbas bai cancanci shugabancin kowace jam’iyyar APC ba.
Mun jima muna faɗar babu wata jam’iyyar Dimokuraɗiyyar da Abdullahi Abbas ya cancanci ya jagoranta balantana APC, a cewarsa.
Ya ci gaba da cewa “Tunaninsa ba na jama’a bane, shi basarake ne a zuciyarsa, kuma sarauta da siyasa ba sa haɗuwa, magana ce ta ƴanci da aƙida, da kuma tsara yadda za a taimakawa talaka, shi kuma yana ganin taimakawa mutane ya ke in yana kula su”.
Labarai masu alaka:
An baiwa Dan sarauniya sabon mukami a gwamnati
Bayan sauke Dan Sarauniya, Ganduje ya nada sabon kwamishina
Wannan dai ya biyo bayan wani martani da shugaban jam’iyyar ya yi kan Ɗan Sarauniyar ya yin da ake rantsar da shi a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na riƙon ƙwarya.
Abdullahi Abbas ya ce, “Ina roƙon mai girma gwamna duk wanda ka bai wa wani muƙami ka auna shi kamar yadda ka auna ciyamomi, domin muna ganin ana kitso da kwarkwata, muna ganin ƴan ƙwaya suna zare idanu, ɗan ƙwaya ya tafi wajen shugabansa mai zare idanu”.
Yanzu haka dai siyasar Kano ta ɗauki zafi, sakamakon samun zazzafar cacar baki tsakanin jagororin siyasar jihar.
You must be logged in to post a comment Login