Labarai
Abin da jama’a da masana ke cewa kan sabbin matakan da Gwamnati ta ɗauka a Zamfara
Al’umma da masana na bayyana ra’ayoyinsu kan sabbin matakai bakwai da Gwamnatin jihar ta sanya don magance matsalar tsaro da ta addabeta.
Matakan dai sun haɗa da rufe kasuwannin jihar da hana hawa babura daga ƙarfe 6 na yamma zuwa 6 na safe da sauransu.
Me jama’a ke cewa game da hakan?
Ga ra’ayoyin waɗansu mazaunan jihar.
Bala Yaro Mada ya ce “Wannan mataki na hana sayar da mai ga jarkoki ko masu babban tanki abu ne da ya dace, kuma ya kamata duk wanda aka kama a masa hukunci”.
“Amma game da hana cin kasuwa abu ne da zai ƙara jefa talakawa cikin raɗaɗi”.
Ita kuwa wata mata da ta nemi a saka sunanta, ta ce “Gaskiya mun ji daɗi saboda matakai ne da ya kamata a ce tuntuni Gwamna ya ɗauka, fatanmu a janyo mata cikin kwamiti ɗin da aka ce an kafa, domin suma zasu bada gudunmuwa”.
Shi ma wani mazaunin Gusau cewa ya yi, “Matakin ya yi daidai domin ƴan ta’adda za su rasa samun biyan buƙatunsu, za su samu ƙarancin mai.
Dr. Sulaiman Shu’aibu Shinkafi ya ce, wannan mataki ne da ya kamata a yabawa Gwamnati kuma ya kamata kowacce jiha su ɗauki irin wannan mataki.
Ita ma wata matashiya ta ce, “Na ji daɗin waɗannan matakai, kuma ina fatan Gwamnan ya sanar da ɗaukar tsatstsauran matakai, a kan duk wanda aka samu na bai wa ƴan ta’adda bayanan sirri.
Gwamnan jihar Muhammad Bello Matawalle, ya roƙi jama’ar jihar su yi haƙuri da halin matsin da za a shiga sakamakon matakan.
Ya ci gaba da cewa, ɗaukar wannan mataki ya zama dole, domin a kare rayuwar al’ummar a jihar.
You must be logged in to post a comment Login