Labarai
Abin da ya sa muka gaza biyan kuɗin jami’an zaɓe – Farfesa Sheka
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSIEC ta yi ƙarin bayani kan rashin biyan ma’aikatan wucin gadi da suka yi mata aiki lokacin zaɓen da ya gabata.
Shugaban hukumar Farfesa Garba Ibrahim Sheka ya ce, halin matsin tattalin arziƙi da ake ciki shi ne ya haifar da tsaiko wajen biyan ma’aikatan.
Sheka ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio da safiyar ranar Alhamis.
A cewar sa, hukumar na jin ba daɗi kan rashin biyan jami’an haƙƙoƙinsu, kuma sun fara biyan wani ɓangaren daga ciki.
Labarai masu alaka:
Rahoto : Ganduje zai kashe fiye da Naira biliyan 2 wajen zaben kananan hukumomin
Siyasar Kano: Mahangar masana kan zaben kananan hukumomi
Ko da aka tambaye shi kan maganar da ya taɓa yi a baya cikin shirin na cewa, Gwamnatin Kano ta basu dukkan kuɗaɗen gudanarwa sai ya musanta hakan.
Sheka ya ce, an bada sahalewar fitar da kuɗin ne ba wai gaba ɗaya kuɗin gwamnati ta biya ba.
A ranar 16 ga watan Janairun da ya gabata ne aka gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin na Kano.
Sai dai har yanzu jami’an wucin gadi da hukumar ta ɗauka suna ci gaba da kokawa kan rashin biyan na su haƙƙoƙinsu.
You must be logged in to post a comment Login