Labaran Kano
Abin da ya sa muka raba gari da mai horaswarmu – Kano Pillars
Ƙungiyar ta Kano Pillars ta ce, rashin shaidar ƙwarewa ta hukumar ƙwallon ƙafa ta Africa ce, ta sanya ta raba gari da maihorarwarta.
Shugaban hukumar gudanarwar ƙungiyar, Alhaji Surajo Shu’aibo Yahaya Jambul ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a ranar Lahadi.
Jambul ya ce, a yanzu ƙungiyar bata da mai horaswa, domin babu wanda ke riƙe da lasisin kwarewa daga hukumar kwallon ƙafa ta Afrika wato CAF, ya kuma godewa tsohon mai horaswar ƙungiyar ta Kano Pillars tare da yi masa fatan alkhairi.
Sai dai a nasa ɓangaren, tsohon mai horarwarta Ibrahim Musu Jugunu ya shaidawa Freedom Radio cewa, har yanzu yana nan a muƙamin shi.
A ranar Asabar ne, ƙungiyar ta sanar da cewa, dama ta samu ga duk mai sha’awar gurbin maihorarwarta.
You must be logged in to post a comment Login