Labarai
Abin da ya sanya ba zamu iya tsayawa Malam Abduljabbar ba – Lauyoyin bada agaji
Kotu ta yi watsi da buƙatar lauyoyin Gwamnati na a bai wa Kwamishinan shari’a na Kano damar bai wa Abduljabbar Nasir Kabara lauyan da zai ba shi kariya.
A zaman kotun shari’ar musulunci ta Ƙofar Kudu na yau ƙarƙashin mai shari’a Ibrahim Sarki Yola, an gabatar da lauyoyi daga hukumar bada agajin shari’a.
Sai dai sun gabatarwa da Kotu bayanai da hujjoji kan cewa ba zasu iya tsayawa domin kare malamin ba.
Daga cikin dalilan, sun ce, suna kare wanda albashinsa bai gaza dubu talatin ba, sannan ba shari’ar da ake zargin ɓatanci ba.
A nan ne kuma lauyan Gwamnati Yakubu Abdullahi ya nemi kotu ta bai wa Kwamishinan shari’a damar ɗaukarwa Malamin lauya.
A ƙarshe Kotu ta yi watsi da buƙatar lauyan Gwamnati, sannan ta umarci a rubutawa wani lauya mai zaman kansa Barista Ɗalhatu Shehu takarda domin ya zama mai kare malamin.
An kuma ɗage shari’ar zuwa ranar 9 ga watan Yunin da muke ciki.
Labarai masu alaƙa:
Abduljabbar ya kori lauyoyinsa
Bayan fitowa daga shari’ar Abduljabbar Nasiru Kabara 03-02-2022
Idan zaku iya tunawa a zaman Kotun na baya, Abduljabbar Nasir Kabara ya raba gari da lauyoyin da suke kare shi a karo na biyu, abin da ya sanya Kotu ta nemi a bashi lauyoyi daga hukumar bada agajin shari’a.
Gwamnatin Kano ce dai ke ƙarar malamin bisa zargin yin kalaman ɓatanci ga manzo (s.a.w), zargin da malamin ya musanta a gaban Kotu.
Kafin a kai ga Kotun dai sai da Gwamnatin Kano ta shiryawa Malamin Muƙabala tare da Malaman Kano wadda aka shafe sama da awanni biyar amma ya gaza kare kansa.
You must be logged in to post a comment Login