Labarai
Abin da ya sanya zamu riƙa tace waƙoƙin yabo – Afakallah
Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano tace ba zata lamunci yadda masu yabon fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w) ke wuce gona da iri ba musamman a cikin waƙoƙinsu na yabo.
Shugaban hukumar Alhaji Isma’il Na’Abba Afakallah ne ya bayyana haka lokacin taron da Madrasatu Ahlu Faidatul Tijjaniyya ta shirya domin nuna rashin goyan bayan ta kan masu yabon dake wuce gona da iri da kuma yin addu’oi kan matsalolin tsaro da suka addabi kasar nan.
Afakallah ya ƙara da cewa lokaci ya wuce da masu yabo zasu riƙa sakin baki kan janibin fiyayyen halitta Annabi (s.a.w) saboda haka hukumar tace fina-finai zata ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen kawo ƙarshen matsalar domin hakan ya sabawa addini.
Na Abba Afakallah yace ya kamata mutane su sani cewa yabon Annabi ibada ce kuma addini ne kuma ya zama dole hukumar ta riƙa ɗaukar kwararan matakai akan duk wanda yake neman wuce gona da iri a cikin yabon Annabi (s.a.w) ta hanyar tace wakokin yabon da ake yi.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya ruwaito shugaban Hukumar Afakallah na yaba wa waɗanda suka ƙirƙiro wannan makaranta domin zata taimaka wajen kawo ƙarshen masu ɓatanci da sunan yabo.
You must be logged in to post a comment Login