Connect with us

Labarai

Abin da zan yi da kuɗin da Ganduje ya bani – Ja’afar Ja’afar

Published

on

Ɗan Jaridar nan Ja’afar Ja’afar ya ce, zai bada kuɗin da Gwamna Ganduje ya ba shi ga shirin Inda Ranka na Freedom Radio domin tallafawa marasa lafiya.

Ja’afar ya shaida wa Freedom Radio cewa zai cika dubu ɗari biyu a kuɗin su zama Naira miliyan guda sannan ya bai wa shirin Inda Ranka.

A ranar Juma’ar nan ne Gwamna Ganduje ya biya Ja’afar Ja’afar Naira dubu ɗari takwas.

Wata kotu a Kano ce ta umarci Gwamnan ya biya Ja’afar ɗin saboda ɓata masa lokaci wajen shari’ar faifan bidiyon Dala.

Ƙarin labarai:

Bidiyon Dala: Ganduje ya biya Ja’afar Ja’afar N800,000 saboda ɓata masa lokaci

Gwamnatin Kano ta yi martani game da ƙorafin Ja’afar Ja’afar kan Ganduje

Shirin Inda Ranka shi ne shirin Rediyon da ya fi tasiri a Arewacin Najeriya, wanda kuma a ciki akan nemi taimako ga masu rashin lafiya da masu neman kuɗin makaranta.

Shirin Inda Ranka da Freedom Radio ke gabatarwa ya sauya rayuwar dubunnan mutane da dama.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!