Labarai
Abin takaici ne zaftarewa ma’aikata albashi – Masu kare hakkin ma’aikata
Kungiyar sasanta matsalolin ma’aikata da walwalarsu ta jihar Kano, ta bayyana cewa sun cimma matsaya da gwamnatin Jihar Kano kan cewar a karshen shekarar da muke ciki gwamnati za ta mayar wa ma’aikata kudaden da aka zaftare musu na albashin watan Mayun da ya gabata.
Shugaban Kungiyar Kwamared Hashim Sale ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio, wanda ya tattauna a kan matasalar da ma’aikata suke fuskanta a wannan lokaci da ake fama da cutar Corona.
Kwamared Hashim Sale ya ce barkewar cutar Corona ta yi sanadiyyar haddasa koma-baya a harkokin yau da kullum na duniya baki daya.
Karin labarai:
Ma’aikatan man fetur sun yi barazanar shiga yajin aiki a Najeriya
Covid-19: Ma’aikata za su koma bakin aiki a Jigawa
Shugaban ya kuma ce hurumin kungiyar ya tsaya ne kan cikakkun ma’aikata, amma banda na wucin-gadi, to amma tana kokarin ganin an mayar da su cikakkun ma’aikata suma nan bada jimawa ba.
Kwamarad Hashim Sale ya kuma yi kira ga ma’aikantan da suka tsinci kansu cikin wannan yanayi da su kara yin hakuri, domin kungiyar na gudanar da aiki ne don ganin an magance wannan matsalar.
You must be logged in to post a comment Login