Connect with us

Jigawa

Covid-19: Ma’aikata za su koma bakin aiki a Jigawa

Published

on

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce ma’aikata za su koma bakin aiki daga ranar Litinin, wanda ya yi dai-dai da ranar shida ga watan Yuli.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ne ya bayyana haka ga manema labarai a fadar gwamnatin jihar.

Gwamnan ya ce ma’aikatan da zasu koma bakin aiki iya yan mataki na 12 kadai ne zuwa sama.

Dangane da batun bude makarantu kuwa gwamna Badaru ya ce jihar Jigawa za ta duba yadda abin zai gudana ba tare da samun matsala ba, yayin da ake cigaba da lalubo hanyoyin magance matsalar annobar Covid-19.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!