Labarai
Abokin Kowa: Babban sufeton ƴan sanda ya yabawa Kanawa
Babban Sufeton Yan sandan kasar nan Alkali Baba Usman ya ce, yanayin hadin kai da ya gani tsakanin gwamnati da jami’an tsaro da kuma al’ummar Kano babbar nasara ce ga ci gaban tsaro.
Sufeton ƴan sandan ya bayyana hakan a ranar Laraba, yayin da ya ziyarci fadar gwamnatin Kano.
Labarai masu alaƙa:
Rundunar ‘yan sandan Zamfara ta ceto mutane 11 da aka yi garkuwa da su
Kano: Ƴan sanda sun kama matasan da ake zargi da kashe abokinsu, dalibin Jami’ar Wudil
Da yake jawabi Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce, duba da yanayin tsaro da ya shiga wani mataki a kasar nan, tuni jihar ta fara amfani da na’urori iri-iri don tabbatar da cikakken tsaro, tare da ganin dazuka basu zama mafakar ƴan ta’adda ba
You must be logged in to post a comment Login