Connect with us

Labarai

Abuja: Yan sanda sun kutsa daji kamo masu garkuwa mutane

Published

on

Jami’an ‘yan sanda a birnin tarayya Abuja, sun cafke wasu da ake zargin cewa masu garkuwa da mutane ne a maɓoyarsu da ke cikin dazuka da wasu tsaunika yankin Apo.

Mai magana da yawun rundunar, SP Josephine Adeh ce ta bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ta fitar yau Laraba.

Sanarwar ta ruwaito cewa jami’an rundunar ƙarƙashin jagorancin kwamishinan ƴan sandan birnin Benneth Igweh, sun kai samame cikin dazuka da ke kewayen shiyyar Zone A da B na unguwar Apo domin tabbatar da tsaro a yankin saboda ana ganin wurin ya zama maɓoyar masu sace mutane.

Ta kara da cewa, Samamen ya haɗa da ƙone gidajen da aka yi ba bisa ƙa’ida ba da dazukan da ke kewayen tsaunuka da kuma tura ƴan sanda su yi rangadi a yankunan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!