Labarai
Abun da yasa ba mu binciki faifan dala ba – Muhuyi Magaji
Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta Kano ta ce dalilin da ya sanya bata binciki zargin rashawa da ake yiwa gwamna Abdullahi Umar Ganduje ba, shi ne rashin samun masu korafi akai.
A wata zantawa da Muhuyi Magajin yayi da Freedom Radio ya ce tun bayan da suka samu korafin, su ka bada cigiyar wadanda suka shigar da shi, domin neman karin bayani wanda kuma har zuwa wannan lokaci basu same su ba.
Muhuyi Magaji ya ce babu wanda ya fi karfin doka, kuma yanzu haka akwai manyan jami’an gwamnatin da suka bincika, bayan da suka samu korafi akan su.
Karin labarai:
Muhuyi zai binciki zargin bidiyon dalar Ganduje
Dalilan da suka sanya Muhuyi zai binciki zargin Ganduje da karbar Na goro
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da aka yi cacar baki kan zaben gwamnan jihar Edo, tsakanin gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje wanda yayi ikrarin zai killace gwamnan jihar Rivers Nysom Wike, inda shi kuma Wike ya yi masa martini da cewar shi ba dala ba ne, ballantana a sunkuma shi a babbar riga.
You must be logged in to post a comment Login