Connect with us

Labarai

ACF ta yi Allah-wadai da cin zarafin da jami’an Amotekun ke yi wa ƴan Arewa

Published

on

Kungiyar Tuntuba Ta Arewa ACF ta yi Allah-Wadai bisa kamawa da, tantancewa da kuma tozarta Mata yan Arewa da ake zargin jami’an tsaron Amotekun na jihar Ondo sun yi, inda ta ce matakin ya saɓa wa kundin Tsarin Mulkin kasar nan, kuma barazana ce ga haɗin kan Ƙasa.

ACF ta bayyana haka ne bayan wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta wanda ake zargin ya nuna jami’an Amotekun su na tsare wasu mata ‘yan Arewa tare da yi musu barazanar korarsu daga jihar Ondo.

A cikin wata sanarwa da shugaban Kwamitin Amintattu na kungiyar, Alhaji Bashir Dalhatu ya sanya wa hannu, ACF ta jaddada cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa kowane ɗan ƙasa ‘yancin zirga-zirga, zama da gudanar da harkokin kasuwanci a ko’ina cikin ƙasar nan ba tare da nuna bambanci ba.

Kungiyar ta nuna damuwa musamman ganin cewa matan da abin ya shafa ana zargin suna gudanar da halastattun sana’o’i, ta na mai gargadin cewa nuna wariya ko tozarta jama’a bisa asali na iya haddasa rashin jituwa tare da kawo barazana ga zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.

ACF ta kuma yi kira ga gwamnatin jihar Ondo da ta gudanar da bincike kan lamarin tare da hukunta duk wani jami’i da aka samu ya karya doka, yayin da ta buƙaci gwamnatin tarayya, hukumomin tsaro da Hukumar Kare Haƙƙin Dan Adam ta Kasa su tabbatar an kare haƙƙin matan da abin ya shafa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!