Labarai
Tsoffin hafsoshin soji sun buƙaci a yi wa tsarin tsaro garambawul

Tsoffin hafsoshin sojin Najeriya kuma abokan aikin marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, sun bukaci da a yi wa tsarin tsaron kasar nan garambawul.
Tsoffin hafsoshin, sun yi wannan kira ne jiya Alhamis yayin wani taron manema labarai da suka gudanar Kaduna wanda Birgediya Janar Isma’ila Abdullahi mai ritaya ya gabatar da jawabi ga manema labarai.
Da ya ke magana yayin taron Brig.-Janar Maharazu Tsiga mai ritaya, tsohon darakta-Janar na hukumar kula da masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), ya yi kira da a ɗauki ƙwararan matakai don magance matsalar rashin tsaro a ƙasar nan.
A cewar sa, ana buƙatar a ƙddamar da dabarun da za a bi don wargaza ayyukansu da kuma dawo da zaman lafiya.
Wanann dai ne zuwa ne bayan rasuwar marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya a hannun wasu ƴan bindiga da suka sace shi a jihar Katsina.
You must be logged in to post a comment Login