Kiwon Lafiya
Adadin masu lalurar tabin hankali na karuwa a Najeriy
Wata sanarwa da shugaban kungiyar likitocin dake kula da masu cutar tabin hankali a kasar Taiwo Obindo ya fitar ta nuna cewa, yanzu haka sama da mutane miliyan 60 ne ke fama da cutar tabin hankali a sassan Najeriya.
Taiwo ya kuma ce, kula da masu fama da lalurar a kasar ya tabarbare ganin yadda alkaluman masu fama da cutar ke karuwa.
A karshe masanin yace, kashi 90 na marasa lafiyar basu da hanyar zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci.
You must be logged in to post a comment Login