Connect with us

Labarai

Adamawa: Immigration ta kama mutane 2 da kuɗi miliyan 34 da ake zargin na yan garkuwa da mutane ne

Published

on

Hukumar Kula da Shige da Fice ta ƙasa ta kama mutane biyu tare da tsabar kuɗi ₦ miliyan 34 bisa zargin alaƙa da masu garkuwa da mutane a Jihar Adamawa.

 

Wannan na cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar reshen Jihar Adamawa, DSI S. Abubakar, ya fitar a ranar Laraba 9 ga Satumba, 2026.

 

Sanarwar ta bayyana cewa, an kama Alhaji Jaye mai shekara 55 da Buba Bello mai shekara 34 ne a ranar Lahadi 6 ga Satumba, 2026, inda aka samu tsabar kuɗi ₦ miliyan 34 a hannunsu.

 

Hukumar ta ce a binciken farko, mutanen sun yi iƙirarin cewa an tanadi kuɗin ne domin biyan kuɗin fansar sakin ɗan’uwan ɗaya daga cikinsu da aka yi garkuwa da shi.

 

Sanarwar ta ƙara da cewa, Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta ƙasa ya bayar da umarnin miƙa mutanen da kuɗin da aka samu a hannunsu ga Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa domin ci gaba da bincike da ɗaukar matakin da ya dace.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!