Connect with us

Labarai

Kotun Tafi-da-gidanka ta Hukumar REMASAB ta hukunta wasu wuraren kasuwanci

Published

on

Kotun Tafi-da-gidanka kan Tsaftar Muhalli ta Hukumar Kwashe Shara ta Kano REMASAB ta hukunta Asibitin Sahara da wasu wuraren kasuwanci a Kano bisa karya ƙa’idojin tsaftar muhalli.

 

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar, Malam Abubakar Ahmad Durumin Iya, ne ya bayyana hakan a wani sakon murya da ya aikewa Freedom.

 

Ya kara da cewa, daga cikin wuraren da aka gurfanar a gaban kotun akwai Sahara Specialist Hospital da ke Hotoro GRA, shagon Gazza Store da ke Hotoro da gidan man TotalEnergies da ke kan titin zuwa Maiduguri, sai kuma gidan man Alaj Petroleum da ke titin zuwa Zariya.

 

REMASAB ta ce an gurfanar da Gazza Store ne bayan gano ruwan roba da lemon kwalba da wa’adin amfaninsu ya ƙare a wurin.

 

Hukumar ta ƙara da cewa, an gargaɗi gidan man Zamson Petroleum da ke titin zuwa Zariya tare da umarnin gyara matsalolin tsaftar muhalli.

 

Abubakar Ahamad Durumin Iya, ya ce, kotun za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta duk mako a faɗin Jihar Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!