Labarai
Rundunar Operation Fansan Yamma ta daƙile yunƙurin satar shanu fiye da 500 a Kaduna

Rundunar Operation Fansan Yamma ta daƙile yunƙurin satar shanu sama da 500 a yankin Rugar Mande Kurmin, Ƙaramar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna, ranar 8 ga Satumba, 2026.
Jami’in Yaɗa Labarai na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya ce sojojin sun ɗauki matakin gaggawa bayan samun kiran neman ɗauki daga mazauna yankin.
Ya ce sojojin sun tare hanyoyin da ake zargin ɓarayin za su bi, tare da kai musu farmaki ta wurare daban-daban, lamarin da ya tilasta musu guduwa suka bar dukkan shanun. Daga bisani an miƙa shanun ga masu su.
Rundunar ta jaddada ƙudurinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da yin kira ga al’umma su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin yaƙar ta’addanci da sauran laifuka.
You must be logged in to post a comment Login