Labarai
Rundunar Yan sandan Bauchi ta kama mutane 2 da ke bai wa masu garkuwa da mutane bayanai

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Bauchi sun kama mutane 2 da ake zargi da bai wa masu garkuwa da mutane bayanai dangane da harin da aka kai a Karamar Hukumar Alkaleri.
Wannan na cikin sanarwar da mai magana da yawun rundunar yan Sandan, SP Nafiu Habib, ya fitar a Litinin din makon nan.
Ya ce harin ya faru ne a ranar 31 ga Yuli, 2026 a kauyen Gwanar Dutse da ke Gundumar Gwana a Karamar Hukumar Alkaleri, inda wani mutum mai shekara 46 ya samu raunin harbin bindiga a cinyarsa ta dama yayin ƙoƙarin tserewa.
Sanarwar ta ce, jami’an ‘yan sanda na Gobirawo sun kama waɗanda ake zargin.
Ya ce, binciken farko ya nuna cewa sun amsa zargin ba maharan bayanai, sannan an miƙa su zuwa Sashen Binciken Laifuka na Jihar Bauchi domin ci gaba da bincike kafin gurfanar da su a kotu.
You must be logged in to post a comment Login