Labarai
ADC ta ankarar da INEC kan amfani da malaman jami’a masu ra’ayin siyasa

Jam’iyyar ADC, ta bukaci Hukumar Zabe ta Najeriya INEC, da ta sake duba batun yin amfani da malaman jami’a da ke da ra’ayin siyasa wajen tattarawa da kuma bayyana sakamakon zaben 2027.
Sakataren Yada Labaran jamiyyar, Bolaji Abdullahi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar. Ya ce jam’iyyar na nuna damuwa ne bayan rahoton cewa sama da manyan malaman jami’a 600 a arewacin Najeriya sun bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Jam’iyyar ta bukaci INEC ta samar da ka’idojin da za su hana jami’an zabe masu nuna bangaren siyasa gudanar da irin wannan aiki, tare da wallafa sunayen jami’an da za ta nada tun kafin zabe domin a gano duk wani rikicin muradun siyasa.
You must be logged in to post a comment Login