Labarai
NUP ta yaba wa Shugaba Tinubu kan fara biyan hakkokin tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways

Kungiyar ‘yan fansho ta Najeriya NUP, ta yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan fara biyan hakkokin tsoffin ma’aikatan kamfanin jiragen sama na Nigeria Airways Naira biliyan 18.
Kungiyar ta ce, kudin zai amfani tsoffin ma’aikata 2,700 da suka shafe sama da shekaru 20 suna jiran hakkokinsu.
Shugaban NUP na ƙasa, Godwin Abumisi, ya ce biyan kudin ya nuna cewa gwamnati ta saurari kiraye-kirayen da kungiyar ke yi na ganin an biya tsoffin ma’aikatan hakkokinsu.
Sai dai kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya ta tabbatar da kammala biyan kudin cikin gaskiya da adalci, tare da sake tantance wadanda ba a kammala batunsu ba, musamman wadanda ke da matsalar bayanan asusun banki. Ta kuma nemi a biya hakkokin wadanda suka rasu ga magadansu bisa ka’ida.
You must be logged in to post a comment Login