Connect with us

Labarai

Ba zamu soke rajistar jam’iyyar ADC ba – INEC

Published

on

Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta yi watsi da bukatar da aka gabatar a kotu domin soke rajistar jam’iyyar ADC da wasu jam’iyyu, tana mai cewa bukatar ba ta cika sharuddan doka da kundin tsarin mulki ba. INEC ta jaddada cewa ikon soke rajistar jam’iyya yana karkashin tsauraran ka’idoji ne, ba wai za a yi shi bisa son rai ko matsin lamba na siyasa ba.

 

Hukumar ta bayyana cewa babu hujjojin da suka nuna jam’iyyar ADC ta karya sharuddan da doka ta tanada, kamar rashin samun kuri’u a zabe ko sabawa ka’idojin rajista. Masana harkokin shari’a sun ce wannan matsayi na INEC zai iya raunana karar sosai, tunda ita ce ke kula da rajistar jam’iyyu a Najeriya.

 

A bangaren siyasa kuwa, wasu sun fassara wannan mataki a matsayin kokarin kare dimokuradiyya daga amfani da kotu domin cimma muradin siyasa. Sai dai Antoni Janar na kasa ya goyi bayan karar, yana mai cewa yawan jam’iyyu marasa tasiri na bata tsarin zabe. Duk da haka, wasu ‘yan adawa sun zargi yunkurin da cewa na siyasa ne domin raunana hamayya. Shari’ar na ci gaba da gudana a kotu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!