Connect with us

Labarai

Hukumar Civil Defence ta cafke mutane 13 da ake zargi da aikata manyan laifuka

Published

on

Hukumar tsaro ta Civil Defence, ta kama mutane 13 da ake zargi da aikata laifukan satar wayoyin wutar lantarki da fashi da makami da kuma satar motoci da safarar mutane.

Jami’in hulda da jama’a na kasa na hukumar, Mataimakin Kwamanda Babawale Afolabi, ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da wadanda aka kama a hedikwatar hukumar.

 

Ya ce, an gudanar da kamen ne a Abuja da jihohin Nasarawa da Plateau da Kogi da Benue da Neja da kuma Kaduna.

 

Ya ce, daya daga cikin wadanda ake zargin, tsohon ma’aikacin kamfanin AEDC mai suna Isaac Zegbe, tare da wasu abokan ta’asarsa da ake zarginsu da lalata sama da kilomita 15 na wayoyin aluminium daga Yangoji zuwa Abaji, wadanda kudinsu ya haura Naira miliyan 350.

Hukumar ta kuma ce, ta kama wasu da ake zargi da fashi da makami, inda ta kwato bindiga kirar AK-47 da harsasai 16 da kuma Naira 70,000.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!