Labarai
ADC ta bayyana sakamakon zaɓen da ta yi a ƙananan hukumomin Kano

Jam’iyyar ADC ta bayyana sakamakon zaben da ta gudanar a ƙananan hukumomin Kano guda arba’in da hudu da ta gudanar.
Jam’iyyar ta ayyana Alhaji Atiku Abubakar a matsayin wanda ya lashe zaben.
ADC ta ce, Atiku Abubakar ya samu kuri’u 155,995 sai kuma Rotimi Amaechi da ya samu kuri’u 9,994, yayin da Alhaji Hayatudeen Usaman ya samu kuri’u 15,914, kamar yadda shugaban kwamitin gudanar da zaben, Dakta John Ayuba ya bayyana wa manema labarai.
Dakta John Ayuba yace zasu tattara sakamakon zabe zuwa hedikwatar su dake Birnin Tarayya Abuja don mika musu sakamakon.
You must be logged in to post a comment Login