Connect with us

Labarai

Kotu ta yi watsi da ƙarar Amaechi kan nasarar Atiku a zaɓen fidda gwani na ADC

Published

on

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da tsohon gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, ya shigar domin ƙalubalantar nasarar tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar ADC.

Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta yanke hukuncin ne bayan lauyan Amaechi, Jibrin Okutepa, ya sanar da kotu cewa ya janye ƙarar saboda ɓangarorin sun sasanta tsakaninsu.

Atiku ya lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar a watan Mayu da ƙuri’u miliyan 1.846, yayin da Amaechi ya samu ƙuri’u 504,117. Tun bayan bayyana sakamakon, Amaechi ya yi zargin cewa an hana wasu damar kaɗa ƙuri’a kuma an tafka kura-kurai wajen gudanar da zaɓen.

A cikin ƙarar da ya shigar, Amaechi ya nemi kotu ta hana Atiku gabatar da kansa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC a zaɓen 2027, sannan ya nemi a hana Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) amincewa da takararsa.

Sai dai bayan sasanci tsakanin ɓangarorin, kotu ta amince da janye ƙarar tare da share shari’ar daga gabanta. Rahotanni sun nuna cewa tun a watan Yuni ne jam’iyyar ADC ta ayyana Amaechi a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa tare da Atiku domin zaɓen 2027.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!