Labarai
An wayi gari da ƙwallewar rana a Saudiyya Yayin da Musulmi ke tsaiwar Arfah

An wayi gari cikin yana yin kwallewar Rana a kasa mai tsarki a daidai lokacin da al’ummar musulmin Duniya kusan miliyan biyu ke gudanar da tsaiwar Arfah.
Tun da sanyin safiya ranar ta kwalle gabanin fara fitowar mafi yawan Alhazai daga tantunan da suka sauka a filin na Arfah da za su tsaya har zuwa faduwar rana.
A zantawar wakilinmu Aminu Umar Shuwajo da wasu Alhazai da suka fara shaida yanayin sun bayyana yadda suke gudanar da ibadar duk da tsananin zafi sakamakon ranar.
You must be logged in to post a comment Login