Labarai
Kotu ta yi watsi da ƙarar da ƙarar neman hana Goodluck tsayawa takarar shugaban ƙasa

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da wani lauya mai suna Johnmary Jideobi ya shigar, inda yake neman a hana tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan tsaya wa takarar shugaban ƙasa a zaɓen baɗi.
Mai shari’a Peter Lifu, yayin da yake yanke hukunci, ya kuma ci tarar Jideobi kuɗi har Naira miliyan 20 domin a bai wa tsohon shugaban ƙasan.
Haka kuma kotun ta ci tarar mai ƙarar Naira miliyan 1 domin a bai wa Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a.
Mai shari’ar ya bayyana cewa Jideobi ba shi da hurumin shigar da ƙarar, domin bai nuna wata asara ko illa da ya sha sakamakon abin da yake zargin Jonathan na son tsayawa takara a zaɓen baɗi ba.
Kafar yaɗa labarai ta TRT, ta ruwaito cewa, alƙalin ya kuma ce wata Babbar Kotun Tarayya da ke Yenagoa da kuma Kotun Ɗaukaka Ƙara sun riga sun yanke hukuncin cewa Jonathan na da damar tsayawa takara, kuma shi ma dole ne ya bi hukuncin kotun ɗaukaka ƙarar.
You must be logged in to post a comment Login